Tantancewar: An Jirkita Labarin
Tushen Magana:
A ranar Litinin, 4 ga watan Janairun shekara ta 2021, masu tantance sahihancin labarai na Cibiyar Bunkasa Demokaradiyya da Cigaba (CDD) sun gano wani labari da jaridu da daidakun mutane suka wallafa cewa Jami’ar Bayero da ke Kano ta soke zangon karatu na shekara ta 2019/2020. Daukar wannan mataki a cewar majiyoyin da suka wallafa labarin ya biyon bayan wani zama ne da majalisar gudunarwar jami’ar ta gudanar ranar Litinin din. Majiyoyin da suka wallafa labarin sun hada da: Daily Nigerian, Daily Trust, Today.ng, Nairaland, Gistmania.
Labarin ya kara da cewa jami’ar ta sanar da ranar 18 ga watan Janairun da mu ke ciki a matsayin ranar da za ta bude makarantar dan cigaba da karatu.
Gaskiyar Al’amari:
Binciken da CDD ta gudanar ya gano cewa Jami’ar Bayeron bat a soke zangon karatu na 2019/2020 ba kamar yadda ake ta yayatawa.
Karin binciken CDD din ya gano cewa sanarwar ko matakin da jami’ar ta dauka shine ba bayyana cigaba da gudanar da al’amuran karatu na zangon 2019/2020 bawai soke shi ba sakamakon targaro da annobar cutar Corona ta janyo.
Daraktan hulda da jama’a na jami’ar, Malam Ahmad Shehu ya bayyana cewa Jami’ar Bayero bata soke kowane zangon karatu ba duk da cewa labarin hakan ya karade dandalin yanar gizo.
Shehu yace a wani zama na musamman da majalisar koli ta jami’ar ta gudanar ranar Litinin, 4 ga watan Janairun shekara ta 2021, ta amince da cigaba da zangon karatun 2019/2020 bayan annobar cutar Corona ta haifar da jirkicewar zangon.
Daraktan hulda da jama’a na jami’ar ya kara da cewa: “bayan cimma matsaya akan yiwa zangon karatun 2019/2020 garanbawul, yanzu dalibai masu karatun digirin farko zasu fara karatun su ranar 18 ga watan da muke ciki kuma su kammala al’amuran karatun su ranar 26 ga watan Afirilun 2021, zasu dawo cigaba da karatu a zango na biyu a ranar 3 ga watan Mayun shekarar nan kuma wannan zango zai kare a ranar 16 ga Satunban wannan shekara”
“dalibai masu karatu mai zurfi wato digiri na biyu da digirin digirgir a cewa jami’ar zasu fara shagulgulan karatu ranar Litinin, 18 ga watan Janairun 2021 kuma su gama ranar Asabat, 5 ga watan Yuni. Zango na biyu ga dalibai masu karatu mai zurfin zai fara ne ranar Ladi, 7 ga watan Yuni yayin da za su kamala ranar Litinin, 11 ga watan Satunban 2021”
Kammalawa:
Labarin da ake yadawa cewa Jami’ar Bayero da ke Kano ta soke zangon karatu na 2019/2020 ba gaskiya bane. Abinda jami’ar tayi shine bayyana cigaban zangon karatun na shekara ta 2019/2020 da ya samu tazgaro sakamakon bullar annobar cutar Corona. Daraktan hulda da jama’a na jami’ar, Malam Ahmad Shehu ne ya tabbatar da cewa ci gaban zangon 2019/2020 ne aka sanar ba soke shi ba.
CDD na jan hankalin jama’a da cewa su rika tantance sahihancin labarai kafin wallafawa ko yada su.
Leave a Reply