Home Fact Check An rage kudin makarantar jami’a ta jihar Taraba da kashi hamsin bisa dari?
An rage kudin makarantar jami’a ta jihar Taraba da kashi hamsin bisa dari?

Hoton wata takarda da ake ikrarin ta samo asali daga ofishin rijista na Jami’ar Jihar Taraba ta zaga kafafun sada zumunta, musamman ma WhatsApp.

Wannan hoton takardar ta sanar da ahalin jami’ar cewa an rage kudin makaranta; wanda za’a wallafar a shekara ta 2022-2023. Takardar ta sanar da cewa gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas, ya bada dama a rage kudin makaranta da kashi hamsin bisa dari.

Bincike:

CDD War Room ta gudanar da bincike akan wannan ikrarin da ake yi, inda ta samo wani bidi’o na Youtube, wanda ya nuna gwamnan jihar yana yiwa dalibai magana a babban dakin taro na makarantar. Ya kuma bayyana wa daliban cewa za’a gudanar da gyare-gyare a dakunan.

A yayin da gwamnan yake neman kujerar a karkashin jam’iyar People’s Democratic Party wato PDP, ya bayyana wa al’umma jajircewar shi akan karatu. Ya kuma yi alkawarin maida karatun firamare da na gaba da firamare kyauta kuma dole. 

Amintattun jaridu da dama a fadin kasar Najeriya su ma sun tabbatar wannan ikrarin, a yayin da suka yiyo rahotanni akan shi a shafukan su na yanar gizo. 

Hukunci: Ikrarin da ake yi akan cewa gwamnan jihar Taraba ya rage kudin makaranta da kashi hamsin bisa dari gaskiya ne. 

Leave a Reply

%d bloggers like this: