Wani mai amfani da shafin sada zumunta na Twitter yayi ikrarin cewa wata sabuwar doka ta ‘yan sanda a Najeriya ta hana mutum fiye da biyu, musamman ma maza, tafiya akan titi a lokaci guda.
“Allah ya so ni kadai na nake yawo na kwanan nan. Sabida ya kamata a bincike wannan sabuwar doka ta ‘yan sanda da ta hana mutum fiye da biyu (maza) tafiya a kan titi da rana tsaka.”
Wannan ya samo asali ne a yayin da wani jami’in ‘yan sanda a Legas mai suna Benjamin Hundeyin, ya tofa albarkacin bakin shi a yayin da wani ya dora wasu bidi’o inda aka ga wasu ‘yan sandan daban suna so su kama wani matashi.
Wannan magana da Hundeyin yayi ya jawo cece-kuce, yayin da wasu suka nuna damuwar su akan kare hakkin bil Adama.
Da’awa: Shin akwai wata sabuwar doka ta ‘yan sanda wannda ya hana mutum fiye da biyu tafiya a lokaci guda?
Bincike: Domin binciko gaskiyar lamarin, CDD Election War Room ta binciko kundin doka ta ‘yan sanda wato ‘Nigeria Police Act 2020’
Sashi na 38 na dokan ya bawa ‘yan sanda daman capke mutane da suke zargi ba tare da takardan shaida daga kotu ba ko kuma ba tare da warrant ba. Duk da haka, sashi na 54 ya hana ‘yan sanda kama mutane sabida yanayin shigar su, ko shekarun su, ko yaren su, ko yanayin tsarin gashin kan su, da dai sauran su.
Bamu samu wani sashi na dokan ba wanda ya baiwa ‘yan sanda daman su capke mutane sabida dalilin cewa suna yawo ko tafiya a kan titi a lokaci guda ba.
Bugu da kari, yayin da muka yi magana da shi Benjamin Hundnyin akan lamarin, ya yi watsi da ikrarin da masu amfani da shafukan sada zumunta suke yi.
Sakamako: Ba gaskiya bane
Ikrarin da ake yi akan cewa akwai wata sabuwar doka na ‘yan sanda wanda ya hana mutum fiye da biyu tafiya a lokaci guda ba gaskiya bace. Binciken mu ya nuna mana wannan bashi da asali a Police Act na 2020. Bugu da kari jami’in ‘yan sanda a Legas ya yi watsi da wannan jita-jita.
